BBC navigation

Vettel bai aikata laifi ba —FIA

An sabunta: 29 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 15:52 GMT
Sebastian Vettel

Gwarzon direban duniya, Sebastian Vettel

Hukumar da ke kula da gasar tseren motoci ta Formula 1, FIA, ta ce ta yi amanna zakaran tseren motoci na duniya Sebastian Vettel bai aikata wani laifi ba yayin gasar Grand Prix ta Brazil.

Tawagar Ferrari ce dai ta rubutawa hukumar ta FIA takarda tana neman bayani a hukumance a kan ko shan gaban Jean-Eric Vergne na tawagar Toro Rosso da Vettel ya yi na bisa ka'ida.

Hukumar ta FIA ta bayyana cewa ta yi amanna wucewar ta Vettel ta halalta amma ba a baiwa Ferrari amsa a hukumance ba tukunna.

Duk wani matakin hukunci da za a dauka ka iya kaiwa ga kwancewa Vettel rawaninsa na gwarzon direban duniya.

In da za a ayyana cewa wucewar ba ta kan ka'ida kuma, to hukuncin da za a yiwa Vettel zai sanya direban Ferrari Fernando Alonso ya zama gwarzon direban duniya.

Sai dai kuma hukumar ta FIA ta yi amanna Vettel bai aikata laifi ba, kuma nasararsa ta uku a jere tana nan daram.

Al'amarin dai yana da sarkakiya saboda bayan da manunan gaban motar Vettel suka bayar sun saba da abin da fitilu da tutocin gefen hanya suka bayar.

Vettel ya sha gaban Vergne ne a zango na hudu na tseren kafin ya kai wurin wata koriyar fitila wadda ke nuna cewa zirin da ba a shan gaba nai ruwan dorawa ya kare. Manunin gaban motarsa kuma ya yi ta nuna alamar gargadi ta tuta mai ruwan dorawa.

Amma kuma hoton bidiyon da ke makale a jikin motar ya nuna alamar wani mai ba da hannu yana daga koriyar tuta gaba da Kwana ta Uku. Vettel ya fara wucewa ne kuma bayan ya wuce tutar.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.