Ferguson ya gargadi 'yan wasansa

Alex Ferguson
Image caption Alex Ferguson ya ce Vidic ba gama murmurewar da zai dawo wasa ba tukunna

Kocin Manchester United Sir Alex Ferguson ya ce wajibi ne 'yan wasansa na baya su kara kwazo idan ba haka su gane kurensu a wasan da za su yi da Man City ranar Lahadi.

Manchester United ta nuna gazawa sosai a wasan da suka yi nasara kan Reading da ci 4-3 ranar Asabar.

Kawo yanzu an zirawa United kwallaye 32 a baki dayan wasannin da suka buga a kakar bana, a don haka ne kuma Ferguson ya ce; "Abin da muwa ne.

"Idan muka taka leda kamar haka ranar Lahadi, to Allah ne kawai ya san abinda zai faru ga remu."

United ce kan gaba a teburin Premier da maki uku, kuma ta samu damar tsallakewa zuwa zagaye na gaba a gasar zakarun Turai tun kafin a kammala wasannin rukunin H.

Sun zira kwallaye 37 - 9 fiye da kowacce kungiya a Premier, sai dai Ferguson yana fargabar 'yan bayansa za su iya shan wuya a hannun Mario Balotelli da Edin Dzeko a lokacin da za su ziyarci filin wasa na Etihad.

Alex Ferguson ya kuma ce Nemanja Vidic bai gama murmurewar da zai dawo wasa ba tukunna, duk da irin matsalolin da yake fama da su a baya.

Karin bayani