'Sunderland na cikin hadari'

Mai horar da 'yan wasan Sunderland, Martin O'Neill

Mai horar da 'yan wasan kulob din kwallon kafa na Sunderland, Martin O'Neill ya ce kulob din na mataki na goma sha bakwai, kuma ya dara kulob din dake mataki na goma sha takwas ne da maki daya kacal.

Hakan inji Mr. ONeill ya sanya Sunderland cikin hadarin barin gasar premier.

A cewar manajan kulob din da aka yi wa lakabi da Black Cats a turance, " Ba na jin zamu kai labari, muddin ba mu samu makin da ake bukata ba. A halin yanzu ba mu da makin da ake bukata kuma abin da ya kamata mu yi kokarin samu kenan."

A wannan makon ne O'Neill zai cika shekara daya da rike mukaminsa na manajan kulob din, kuma ya yi matukar kokari wajen ganin kulob din bai fita daga gasar ta premier ba, bayan ya karbi ragamar Sunderland daga hannun Steve Bruce a kakar wasannin bara.

"Matsayin da muke ciki yanzu na nuna cewa sai munyi da gaske." Inji O'Neill.

Ya bayyana fatan cewa " Halin da muke ciki tamkar wata fafatawa ce a gare mu kamar yadda muka yi a bara, kuma ina fatan abin da ya faru a bara zai zama darasi mai kyau ga 'yan wasanmu.