Rugby: Ingila za ta hadu da Wales

New Zealand

Mai masaukin baki Ingila za ta kara da Wales da kuma Australia a rukunin A a gasar cin kofin duniya ta kwallon zari-zuga (Rugby) da za a yi a shekara ta 2015.

Scotland za ta fafata a rukunin B da Afrika ta Kudu da kuma Samoa.

Ita kuwa Ireland za ta hadu ne da Faransa da Italiya a rukunin D.

Masu rike da kanbun New Zealand na rukunin C ne, inda za su fafata da Argentina da Tonga.

Za a fara gasar ne a ranar 18 ga watan Satumba na 2015, yayin da za a buga wasan karshe a Twickenham ranar 31 ga watan Oktoba.