Eriksson na kan hanyar zama kocin Ukraine

Image caption Tsohon Kocin Ingila, Sven Goran Eriksson

Hukumar Kwallo kafa ta kasar Ukraine ta ce tana tattaunawa da tsohon Kocin Ingila Sven-Goran Erikson domin bashi ragwamar gudanar kungiyar kwallon kafa ta kasar.

Wata mai magana da yawun hukumar tace '' an riga an yi masa tayi kuma tattaunawa ta kankama''.

Kafin hakan dai Ukraine ta nemi wani kocin club din Ingila Harry Rednapp da irin wannan tayin, amma daga karshe Redknapp ya karbi aikin jagorancin kungiyar kwallon kafa ta Queen's Park Rangers.

Eriksson mai shekaru 64, shi ne mai horarda 'yan wasan kungiyar kwallon kafa ta BEC Tero ta kasar Thailand tun watan Satumba, kuma ya jagoranci kungiyoyin kwallon kafa na AS Roma, da manchester City da kuma Benfica.

Tsohon kocin kungiyar kwallon kafar ta Ukraine, Oleg Blokhin, yayi murabus ne a karshen watan Satumba bayan kungiyar ta kasa wuce matakin share fage na gasar cin kofin Nahiya Turai wadda Ukraine ta karbi bakunci a bana.

Karin bayani