West Ham za a baiwa Olympic Stadium

Image caption Tambarin kungiyar kwallon kafa ta West Ham United

An bayyana sunan kulob din West Ham United a zaman wanda zai karbi filin da aka yi wasannin Olympics na shekara ta 2012 a London.

Hukumar da ke kula da filin, London Legacy Development Corporation (LLDC) ita ta zabi Kulob din wanda ke buga wasa a gasar Premier a zaman na daya daga cikin wadanda suka yi tayin karbar filin, bayan wata ganawa ranar Laraba.

Ana sa ran a sake bude filin wasan wanda ya lashe Fam miliyan 429 gaba daya kafin watan Agusta na 2015.

Da wannan dai yanzu West Ham zai sauya mazauninsa da tazarar mil biyu daga filin wasanshi na Upton Park mai daukar 'yan kallo 35,000 zuwa sabon filin mai daukar 'yan kallo 60,000.

Karin bayani