Ferguson ya yaba wa 'yan wasan Man U

Manajan Manchester United, Sir, Alex Ferguson
Image caption Manajan Manchester United, Sir, Alex Ferguson

Sir, Alex Ferguson ya bayyana kayen da Manchester City ta sha a hannun Manchester United, da cewa nasara ce ta musamman.

An dai tashi wasan, Man U na da ci uku, yayin da Man City kuma ke da ci biyu.

Game da karawar kuloblukan biyu a karo na 31 a gasar Premier League, manajan Man United ya ce " Kai anyi wasa mai kyau, wasan na musamman ne "

"Wasan ya kayatar, kuma yana nuna irin karfin da gasar ta Premier League ke da shi.

Rabon da a doke Man City a filin wasa na Etihad, tun karawarsu da Everton a watan Disembar shekarar 2010.

'Yan wasan dai sun burge Furguson, musamman ma dan wasan gaba Wayne Rooney.