Ba mu ji wata kunya ba - Wenger

Bradford
Image caption Bradford dai tana matakin League na biyu ne a Ingila

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya ce kulob din bai ji wata kunya ba bayan da kungiyar Bradford da ke matakin League na biyu ta fitar da su daga gasar cin kofin Capital One Cup.

Arsenal ta sha kashi ne da ci 3-2 a bugun fanareti bayan da aka tashi 1-1 a filin wasa na Coral Windows.

"Mun yi duk abinda ya kamata a mintina na 120, a don haka dole mu yaba wa Bradford," a cewar Wenger.

"Za ka ji kunya ne kawai idan baka taka rawar gani ba, ina ganin za su fi damuwa da kuma jin kunya."

Wenger ya yi amfani da kwararrun 'yan wasa sai dai sun kasa nuna kwarewarsu kan 'yan wasan na Bradford.

Sai a minti na 88 sannan suka samu damar farke kwallon da aka zira musu ta hannun Thomas Vermaelen, bayan da tun farko Garry Thompson ya zirawa masu masaukin bakin kwallonsu.

Sai dai Wenger ya ki yarda ya soki 'yan wasansa, wadanda wasa daya kawai suka lashe a cikin shida da suka buga na bayan-bayan nan.