Ana tuhumar Barry da laifin rashin da'a

Gareth Barry
Image caption An samu rudani sosai bayan kammala wasan

Hukumar kwallon kafa ta Ingila na tuhumar dan wasan tsakiya na kulob din Manchester City Gareth Barry da laifin rashin da'a.

Tuhumar na da alaka da wani abin da ya faru, bayan an biyo City har gida an doke ta a karawar da suka yi da Manchester United.

Hukumar dai ta dau matakin ne a karkashin doka ta E3 wacce ke hani da furta kalaman cin mutunci ko zagi ga jami'an da ke sa ido a wasa.

Barry, dan shekaru 31 na da nan da karfe bakwai na daren ranar Alhamis ya mayar da martani game da tuhumar da ake masa.

Robin Van Persie ne ya jefa kwallo a ragar City a karin lokacin da aka yi, wanda ya baiwa kulob dinsa nasara.

Sai dai halayyar 'yan kallo bayan kammala wasan ita ce ta fi daukar hankali.

Mai tsaron gidan City, Joe Hart ma ya yi kokarin hana wani dan kallo rugawa cikin filin wasa don cimma Rio Ferdinand.

Bayan kammala wasan dai 'yan sanda sun tuhumi wasu mutane tara, ciki har da wani wanda ake zargi da ingiza mutane domin nuna banbancin launin fata.

Yayin da biyu daga cikinsu kuma aka tuhume su da shiga filin wasa ba bisa ka'ida ba.