Bitar al'adu ga 'yan kasashen waje

Luis Suarez
Image caption An dakatar da Suarez wasanni 8 bara kan kalaman wariyar launin fata

Hukumomin kula da kwallon kafa na duba yiwuwar saka darusan karantar da al'adun gargajiya ga 'yan wasan kasashen waje domin yakar aikata laifukan da ke da alaka da kabilanci a fagen wasannin Ingila.

BBC ta fahimci cewa hakan na cikin wani martani ga bukatar da Fira Minista David Cameron ya gabatar a farkon bane ne, cewa a tsaurara matakai domin yakar kabilanci a fagen wasan kwallon kafa.

Shirin da ke kunshe a cikin shafuka 93, an kira shi da 'shirin yakar bambancin launin fata a kwallon Ingila'.

Ya kuma hada da bukatar a tilasta wa kungiyoyi su sanya dokar yaki da bambancin launin fata a kwantiragin da 'yan wasa da manajoji suke sanya hannu a kai.

Duk da cewa kungiyoyi nada nasu ka'idojin wurin tunkarar batun wariyar launin fata, amma baya cikin tsarin kwantiragin da manajoji da 'yan wasa ke sanya wa hannu.

Sai dai wannan shirin na bukatar sabbin 'yan wasan da ke shigo wa Ingila su samu horo kan yanayin al'adun Burtaniya (British cultural environment) lamarin da ake ganin zai ja hankali.

Wannan mataki dai wani martani ne ga lamarin bambancin launin fatar da ya faru a bara da dan wasan Liverpool Luis Suarez.

An dakatar da shi wasanni takwas saboda furta kalaman wariyar launin fata ga dan wasan Manchester United Patrice Evra.

Karin bayani