Romeu zai shafe wata shida yana jinya

Oriol Romeu
Image caption Oriol Romeu zai shafe watanni shida baya taka leda

Dan wasan tsakiya na Chelsea Oriol Romeu zai shafe watanni shida yana jinya bayan da aka yi masa tiyata a gwiwarsa.

Romeu, mai shekaru 21, an yi masa tiyata ne a ranar Litinin.

Dan wasan na kasar Spain ya samu rauni ne a wasan da Chelsea ta doke Sunderland da ci 3-1 ranar Asabar a gasar Premier ta Ingila.

Daga nan ne kuma ya dawo London mai makon tafiya Japan tare da sauran tawagar Chelsea domin halattar gasar cin kofin zakarun duniya.

Ya bugawa Chelsea wasanni 33 tun bayan da suka sayo shi daga Barcelona a fan miliyan 4 da rabi a watan Agustan 2011.

Ganin yadda aka dakatar da Mikel Obi wasanni uku, ga Mikel Essien ya tafi aro zuwa Real Madrid, koci Rafel Benitez na fuskantar matsin lamba kan 'yan wasan tsakiyar da zai yi amfani da su.

Karin bayani