Kofin Zakarun duniya: An doke Al Ahly

Image caption Paolo Guerrero lokacin da ya tuna kwallo zuwa cikin ragar Al Ahly

Zakarar kungiyoyin kwallon kafa a nahiyar kudancin Amurka, Corinthians ta samu gurbin farko a wasan karshe na gasar cin kofin duniya ta zakarun kungiyoyi da doke zakarar kungiyoyin Afrika, Al Ahly a wasan gab da karshe da suka buga ranar Laraba a birnin Tokyo na Japan.

Kungiyar ta kasar Brazil ta doke takwararta daga Masar ne da ci 1-0 bayan da Paolo Guerera ya jefa kwallo a ragar Al Ahly a minti na talatin na wasan.

Al Ahly dai ta kusan rama cin sakamakon zafafan hare-hare daga Ramy Rabia da Wali Sulaiman bayan dawowa hutun rabin Lokaci.

Da wannan dai Corinthians za ta buga wasan karshe na gasar da kungiyar da ta lashe wasan gab da karshe ta biyu tsakanin Chelsea ta Ingila da kuma Monterry ta Mexico.

Karin bayani