Mai yiwuwa ba za a hukunta Liverpool ba

Image caption 'Yan wasan Liverpool suna murnar lashe kofi

Hukumar shirya gasar Premier na duba yiwuwar yin watsi da batun bincikar neman da Kulob din Liverpool ya yi wa dan wasan Fulham Clint Dempsey ba tare da sanin Fulham din ba.

Wannan dai ya biyo ne bayan rokon gafarar da Kulob din na Liverpool yayi ga Fulham.

Kulob din na Fulham ne ya shigar da koke gaban hukumar a watan yuli bayan wani labari ya bayyana a shafin internet na Liverpool da ke ikrarin cewar Dempsey ya koma Liverpool.

Sai dai Manaja daraktan Liverpool Ian Ayre yanzu ya rubuta takardar neman afuwa ga shugaban Fulham Muhammed Alfayed bisa labarin da aka an saka shi ne bisa kuskure.

Yanzu dai hukumar za ta duba batun; yayin da akwai yiwuwar ta rufe maganar, akwai kuma yiwuwar Liverpool za ta fuskanci horo idan hukumar tace ta karya kaidojin daukar dan wasa.

Karin bayani