An gama zaben gwarzon dan kwallon BBC

Zaben gwarzon dan kwallon BBC
Image caption Za a bayyana sakamako ranar 17 ga watan Disamba

An kammala zaben gwarzon kwallon Afrika na BBC na shekara ta 2012.

Za a bayyana sakamako ranar 17 ga watan Disamba a shirin labarin wasanni na sashin Turanci na BBC Sport Today da misalin karfe 4.30 agogon GMT wato 5.30 agogon Najeriya da Nijar.

'Yan wasa biyar ne suka samu shiga cikin takarar, da suka hada da Yaya Toure, takwaransa na Ivory Coast Didier Drogba, dan Senegal Demba Ba, da Younes Belhanda na Morocco da kuma Christopher Katongo na Zambia.

Wannan dai shekara ce da dukkan 'yan takarar suka taka rawar gani, inda hudu daga cikinsu suka lashe lambobin yabo.

Nasarorin 'yan wasan

Drogba ya ci fanaretin karshe da ya baiwa Chelsea damar lashe gasar cin kofin zakarun Turai a karon farko a tarihin kulob din, sannan ya zura kwallon da ta taimaka musu suka lashe gasar kofin FA.

Takwaransa na Ivory Coast Yaya Toure, ya tallafawa Manchester City wurin lashe gasar Premier League a karon farko cikin shekaru 44.

Shi ma Belhanda ya lashe gasar Ligue 1 ta Faransa inda ya zira kwallaye 12 da suka taimakawa Montpellier samun nasara a karon farko cikin kusan shekaru 100 da kafa kulob din.

A matakin kasa-da-kasa kuwa, Katongo ya jagoranci Zambia ta lashe gasar cin kofin kasashen Afrika, inda suka doke Ivory Coast a bugun fanareti.

Demba Ba bai taka rawar gani a gasar cin kofin Afrika ba, inda aka fitar da Senegal a zagayen farko, sai dai ya taka rawar gani a Newcastle, inda suka kare kakar wasannin bara a mataki na biyar tare da zira kwallaye 17.

Karin bayani