Chelsea ta kai wasan karshe a Japan

'yan wasan chelsea
Image caption 'Yan wasan Chelsea

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta soma gasar cin kofin Zakarun Duniya da kafar dama inda ta sami nasara a kan kungiyar Monterrey ta kasar Mixico da ci 3-1 a wasan kusa da na karshe da aka yi ranar Alhamis.

Juan Mata ne ya fara sakawa Chelsea kwallonta ta farko a minti 17 kafin daga bisani Fernando Torres ya jefa ta biyu bayan an dawo daga hutun rabin lokaci a minti 46, sannan kuma Darvin Chavez na kungiyar ta Monterrey ya ci kansu a minti 48, ana shirin tashi a minti na 90 Aldo de Nigris ya jefawa Monterrey kwallonta daya.

Da wannan nasara da Chelsean ta samu yanzu zata hadu da kungiyar Corinthians ta Brazil , wadda ta fitar da Al Ahly ta Masar da ci 1-0 a daya wasan kusa da na karshen.

A ranar Lahadi ne Chelsean zata kara a wasan karshe da Corinthians din, yayin da ita kuma kungiyar Corinthians zata fafata da Al Ahly domin neman matsayi na uku.

Karin bayani