'Magoya baya ba dabbobi ba ne'

Vincent Kompany
Image caption Vincent Kompany yana taka rawar gani sosai a Man City

Kyaftin din Man City Vincent Kompany ya yi watsi da ra'ayin sanya raga tsakanin 'yan wasa da masu kallo, saboda a cewarsa kada a daukesu 'kamar wasu dabbobi'.

An jefi dan wasan Manchester United Rio Ferdinand da wani abu lokacin da yake murnar nasarar da suka yi da ci 3 da 2 a kan Man City ranar Lahadi.

Sakamakon haka ya sa kungiyar kwararrun 'yan wasa ta PFA, ta yi kiran da a sanya kariya a filayen wasanni.

"Ina fatan cewa za a dauki mataki, amma kada a manta daga ina wasan kollon kafa ya samo asali, sannan kuma wanne mataki ya kawo yanzu?

An tuhumi mutane 9 bayan kammala wasan, haka kuma jama'a sun rinka jifan dan wasan gaba na Manchester United Wayne Rooney.

Hakan kuma ya kaiga Kompany, mai shekaru 26 dan kasar Belgium, wanda bashi da tabbas din buga wasan da City za ta yi da Newcastle a karshen mako saboda raunin da yake fama da shi, yin Allah wadai da abinda ya wakana a filin wasa na Etihad.

"Duka dai wannan ba abin alheri bane ba ga Manchester City ko Manchester United, harma ga wasan kollon kafa", kamar yadda Kompany ya shaida wa shirin BBC na Turanci Football Focus, lokacin da City suka kai ziyarar shekara-shekara a asibitin Yara na Royal Manchester.

Karin bayani