Wiggins na son kare kambinsa na tsere

bradley wiggins
Image caption Bradley Wiggins

Bradley Wiggins na son kare kambinsa na zakaran tseren keke na gasar Tour de France duk da shirin kungiyarsa ta SKY na maye gurbinsa na jagoran 'yan wasanta da Chris Froome a gasar ta 2013.

Wiggins dan shekara 32 wanda Froome ya mara masa baya ya sami nasarar zama zakaran gasar ta tseren kekunan ta Faransa na Birtaniya na farko ya ce zai hakura da duk matakin da kungiyar tasa ta dauka.

Sai dai a wata hira da ya yi da BBC, wiggins ya ce, yana ganin zai yi kokari ya sake zama zakaran gasar amma bai sani ba ko za a sami jagorori biyu ne na kungiyar a gasar.

Dangane da wannan kalami na Wiggins ana ganin idan kungiyarsa ta SKY , ba ta yi amfani da wannan shawara da ya kawo ba ta sanya jagorori biyu a gasar ba wata kila ba zai amince ya karbi matsayin mai mara baya ga Froome ba.

Ana ganin Froome, zai fi iya taka rawar a-zo-a-gani a gasar ta tseren na Faransa na 2013 sabo da irin hanyoyin da za abi masu wahala.

Froome haifaffen kasar Kenya shi ne ya zo na biyu a gasar ta wannan shekara ta 2012, kuma ana ganin yafi Wiggins kokari a hanyoyin da suka ratsa tsaunuka, wanda kuma gasar ta 2013 ta kunshi irin wadannan hanyoyi.