Chelsea ta kasa zama zakarar Duniya

Image caption Paolo Guerera shi ne ya baiwa Corinthians kambin wannan shekarar

Kungiyar Kwallon kafa ta Corinthians da ke Brazil ta lashe kofin zakarrun kungiyoyin kwallon kafa na duniya bayan doke Chelsea da ci 1-0 a wata karawar karshe da aka yi kare-jini-biri-jini ranar Lahadi.

Dan wasan gaba Paolo Guerero ne ya jefa kwallon daya tilo a minti na 69 na wasan wadda aka buga a filin wasa na birnin Yokohama dake Japan.

Wasan dai ya kasance ta in-baka-yi-bani-wuri tun daga busa usur na farko har zuwa na karshe inda duka bangarorin biyu suka yi barar da damammakin cin wasan yayin da kwallo ke fita daga wannan bangaren ta fada wancan.

Chelsea ta zo gab da fara cin wasan a minti na takwas in ban da golan Corinthians Cassio ya buge wani jefa kwallo daga Gary Cahil a wani yanayi da ba saban ba.

Wannan dai shi ne karo na biyu da kungiyar ta birnin Sao Paolo ta lashe kambin gasar ta zakarun kungiyoyin duniya.

Karin bayani