Peter Ndlovu yayi hadarin mota

Image caption Peter Ndlovu tsohon dan wasan Zimbabwe

Tsohon dan wasan Coventry ya samu mummunan rauni a cikin wani hadarin mota a kasar sa Zimbabwe.

Hadarin wanda ya afku a yankin Victoria Falls ya yi sanadiyyar mutuwar yayansa Adam, wanda shi ma wani kwararren dan wasan Kwallon kafa ne.

Mutanen biyu na tafiya ne zuwa wajen wani wasan sada zumunci tsakanin Highlanders Legend da kuma wata kungiyar dake yankin na Victoria Falls.

Motar dai ta kwace ne daga hannun matukin ta, ta saki hanya inda bugi wata bishiya.

Ndlovu mai shekaru 39 shi ne mataimakin kocin kungiyar kwallon kafa ta kasar Zimbabwe wadda ya bugawa wasa har sau 100, kuma shine babban kocin kungiyar kwallon kafa ta 'yan kasa da shekaru 23 ta kasar.

Karin bayani