Zan cigaba da zama a Arsenal - Wilshere

Image caption Dan wasan tsakiya na Arsenal da Ingila Jack Wilshere

Dan wasan tsakiya na Ingila Jack Wilshere ya ce ya na kusa da sa hannu kan wata sabuwar yarjejeniya da Kulob din sa na Arsenal.

Wilshere ya ce yana tattaunawa da Club din kuma ga alamu zai tabbatar da cigaba da kasancewa a can, a cikin 'yan makonni masu zuwa.

Dan wasan mai shekaru 20 wanda ya dawo wasa kungiyar a watan Oktoba bayan kwashe watanni 15 yana jinyar rauni, ya ce ya tabbata Arsene Wenger shi ne yafi kowa dacewa ya jagoranci kungiyar.

Wilshere dai bai samu buga wasa ko daya ba a duk tsawon zangon wasannin da ya wuce saboda samun karaya a wuyan kafar sa da yayi lokacin da Arsenal ke buga wani wasan sada zumunci da kungiyar Red Bulls da ke birnin New York a watan yuli na shakarar 2011

Karin bayani