Balotelli ya kai karar Man City

mario, balotelli
Image caption Mario Balotelli, bai amince da hukuncin da City ta yi masa ba

Dan wasan Manchester City Mario Balotelli ya kai karar Kungiyarsa gaban Kotun Gasar Premier, kan hukuncin da ta yanke masa na cin tararsa albashinsa na sati biyu sabo da abubuwan rashin da'ar da ya aikata a kakar wasannin da ta wuce.

Dan wasan mai shekaru 22 bai buga wasanni 11 ba na cikin gida da kuma tsakanin wasu kungiyoyin kasashen Turai sabo da dakatarwar da aka yi masa daga buga wasanni.

Balotelli ya daukaka kara a kan hukuncin da kungiyar ta yi masa amma kuma wani kwamiti mai zaman kansa da kungiyar ta kafa a kan hukuncin shi ma ya amince da hukuncin.

Ana saran dan wasan zai bayyana tare da lauyansa dan Italiya da kuma wakili daga kungiyar 'yan wasan kwallon kafa kwararru ta Ingila, yayin da ita kuma kungiyar Manchester City zata je da lauyoyinta.

Tarar sati biyu shi ne mafi tsananin hukuncin da kungiyar za ta ci dan wasa kamar yadda kwantiraginsa ya tanada, ko da ike dai kungiyar ta City ta ki ta ce uffan a kan batun amma tana ganin zata sami nasara a shari'ar.

Ba kasafai dai ake samun irin wannan rikici tsakanin dan wasa da kungiyarsa ba da har lamarin kan kai ga Kotun Gasar Premier.

Jumulla dai an baiwa dan wasan katin gargadi 9 da kuma na kora 3 a kakar wasannin da ta gabatan, kuma kungiyar ta City ta fara shirin hukunta dan wasan ne tun lokacin da aka kore shi a wasansu da Arsenal a watan Aprilu na wannan shekara ta 2012.