Rory Mcllroy ne zakaran Golf na duniya

rory, mcllroy
Image caption Rory Mcllroy ne na daya a Golf a duniya Rory Mcllroy dan Yankin Arewacin Ireland ya kammala shekarar 2012 a matsayin na daya a wasan Golf a duniya bayan da ya zama na daya a jerin 'yan wasan Golf din a Turai da Amurka. Zakaran gasar PGA ta Amurka, ya kammala shekarar a jerin zakaru hudu, inda Luke Donald ke bi masa baya sai Justin Rose na uku, yayin da Tiger Woods wanda ya taso daga matsayi na 23 a farkon shekaran nan ta 2012 ya zama na hudu. Jumulla akwai 'yan kasashen Turai 19 a cikin jerin fitattun gasar na duniya 50, da Amurkawa 4 ke cikin goma na farko. Dan wasan da ya fi gamuwa da koma baya a shekarar shi ne Lee Westwood wanda ya fado daga matsayi na 2 a duniya zuwa na 7 a cikin watanni 12 da suka wuce. Shi dai Westwood sau daya ya sami nasara a lokacin a gasar kwararru ta Scandinavian. Mcllroy ya sami nasara a gasa dai-dai-dai-dai har guda biyar a shekarar ta 2012. Mcllroy dan shekara 23, shi ne dan wasa mafi karancin shekaru da ya sami nasarar zama zakaran gasar PGA ta Amurka tun bayan Tiger Woods da ya yi wannan bajinta a 1998. Rory Mcllroy, matashi na biyu da ya taba zama zakaran gasar PGA ta Amurka bayan Woods.

Rory Mcllroy dan Yankin Arewacin Ireland ya kammala shekarar 2012 a matsayin na daya a wasan Golf a duniya bayan da ya zama na daya a jerin 'yan wasan Golf din a Turai da Amurka.

Zakaran gasar PGA ta Amurka, ya kammala shekarar a jerin zakaru hudu, inda Luke Donald ke bi masa baya sai Justin Rose na uku, yayin da Tiger Woods wanda ya taso daga matsayi na 23 a farkon shekaran nan ta 2012 ya zama na hudu.

Jumulla akwai 'yan kasashen Turai 19 a cikin jerin fitattun gasar na duniya 50, da Amurkawa 4 ke cikin goma na farko.

Dan wasan da ya fi gamuwa da koma baya a shekarar shi ne Lee Westwood wanda ya fado daga matsayi na 2 a duniya zuwa na 7 a cikin watanni 12 da suka wuce.

Shi dai Westwood sau daya ya sami nasara a lokacin a gasar kwararru ta Scandinavian.

Mcllroy ya sami nasara a gasa dai-dai-dai-dai har guda biyar a shekarar ta 2012.

Mcllroy dan shekara 23, shi ne dan wasa mafi karancin shekaru da ya sami nasarar zama zakaran gasar PGA ta Amurka tun bayan Tiger Woods da ya yi wannan bajinta a 1998.

Karin bayani