Dokar hana wariyar launin fata a Rasha

magoyabayan, zenit
Image caption Magoya bayan Zenit, masu adawa da 'yan wasa bakaken fata da 'yan luwadi.

Gwamnati da kuma Hukumar Wasan Kwallon Kafa na Rasha na tattauna sabbin dokokin da zasu hana magoya bayan kungiyoyin wasa kiran hana kungiyoyin daukar 'yan wasa bakaken fata da 'yan luwadi.

Hakan dai ya biyo bayan kara tababar cancantar Rashan ta karbar bakuncin gasar cin Kofin Kwallon Kafa na Duniya ta 2018 da ake yi ne,sakamakon kiran da kungiyar magoya baya mafi girma ta kungiyar kwallon kafa ta Zenit da ke Saint Petersburg ta yi na klub din kada ya dauki 'yan wasa bakar fata da 'yan luwadi.

A kan hakan sakataren kungiyar 'yan wasan kwallon kafa da masu horad da 'yan wasa na Rasha, Nikolai Grammatikov, ya ce dukkanin 'yan wasa musamman ma bakaken fata ya kamata su sake shawara game da yin wasa a kasar.

Ya ce wannan ba shi ne karon farko da hakan ke faruwa ba a Rashan, kuma hakan na bata sunan kasar ne kawai, wadda zata karbi bakuncin gasar Kofin Duniya ta 2018.

Karin bayani