Kocin Najeriya na bin bashin albashi

stephen keshi
Image caption Stephen Keshi, yana bin bashin albashin watanni biyu 'yan kwanaki kafin gasar kofin Afrika.

Hukumar kwallon Kafa ta Najeriya,NFF, ta bayyana cewa kocin kungiyar wasan kasar, Super Eagles, Stephen Keshi yana binta bashin albashin watanni biyu, watanni biyu kafin fara gasar cin Kofin Kasashen Afrika.

Bayan albashin ma, shekara daya da kama aikinsa har yanzu hukumar ba ta ba Keshin motar hawa da gidan da za ta bashi kamar yadda yake a yarjejeniyar kwantiraginsa ba.

Har yanzu kocin bai fito fili ya bayyana korafinsa game da lamarin ba ga hukumar, kuma yana cigaba da shirye-shiryen tunkarar gasar Kofin Afrikan da za a yi a Afrika ta Kudu daga ranar 19 ga watan Janairu mai kamawa zuwa 10 ga watan Fabrairu na shekarar mai zuwa.

Hukumar kwallon kafar ta Najeriya wadda ita ce ke da alhakin daukar masu horad da 'yan wasa na kasar da kuma biyan su albashi, ba ta biya mataimakan kocin ba, Daniel Amokachi da Sylvanus Okpala da kuma Ike Shorunmu albashin watanni.

Shugaban Hukumar Kwallon ta Najeriya, Aminu Maigari ya ce suna sane da lamarin kuma suna kokarin ganin an baiwa masu horad da 'yan wasan dukkanin hakkokinsu.

Wannan dai ba shi ne karon farko da ba a biya masu horad da 'yan wasan Najeriya albashi ba, domin a baya bayan nan tsoffin kociyoyin kasar irin su Christian Chukwu da Shuaibu Amadu da Samson Siasia da Austin Eguavoen da John Obuh da kuma Eucharia Uche sun nemi a biya su bashin albashinsu da suke bin hukumar.

Najeriyar tana shirin yin wasan gwaji da Catalonia inda zata yi amfani da 'yan wasan cikin gida ranar 2 ga watan Janairu, kuma daga cikinsu ne za a zabi wadan da za a sa cikin jerin 'yan wasan kasar 23 da za su yi mata gasar cin Kofin Afrika.

A ranar 21 ga watan Janairu ne Najeriyar zata fara gasar inda za ta yi wasa da Burkina Faso sannan kuma ta kara da Zambia da kuma Habasha a rukuni na uku, wato Group C.