Yaya Toure ne zakaran kwallon Afrika na Caf

Yaya Toure
Image caption Yaya Toure yana taka rawar gani a Man City da Ivory Coast

Dan wasan kasar Ivory Coast da Manchester City Yaya Toure ya lashe kyautar zakaran Dan Kwallon Afirkan CAF a karo na biyu a jere.

Dan uwansa dan Ivory Coast Didier Drogba ne ya zo na biyu a gasar zakaran kwallon na Afirka wadda hukumar kula da kwallon kafa ta Afirka ke shiryawa.

Yayin da Alexandre Song na Kamaru ya zo na uku.

Toure, mai shekaru 29, ya lashe kyautar ne bayan da ya samu kuri'u mafiya yawa da kociyoyin kwallon kafa na kasashen Afrika suka kada.