Saura kiris a hallaka Van Persie - Ferguson

Van Persie
Image caption Van Persie da Williams sun yi hatsaniya sosai kan lamarin

Kocin Manchester United Sir Alex Ferguson ya ce Robin van Persie "ya tsallake rijiya da baya" bayan da Ashley Williams na Swansea ya buga masa kwallo a baya, a wasan da suka tashi 1-1.

Van Persie na kwance a kasa lokacin da Williams ya buga kwallo a kansa daf-da-daf, duk da cewa alkalin wasa ya nemi a dakatar da kwallo a lokacin.

Ferguson na ganin Van Persie ya yi nasarar kaucewa wani mummunan rauni.

"Robin van Persie ya tsallake rijiya da baya. Wannan mummunar dabi'a ce daga dan wasansu," kamar yadda Ferguson ya shaida wa BBC.

"Ya kamata hukumar FA ta dakatar da shi. Robin zai iya karya wuya."

Kocin na United ya ce Williams, mai shekaru 28, ya buga kwallon ne da gangan a kan Van Persie, wanda ya mayar da martani cikin fushi - alkalin wasa Michael Oliver ya gargadi duka 'yan wasan biyu.

Karin bayani