Mahaifiyar Andy Murray ta masa hasashen nasara a 2013

Andy Murray
Image caption Zakaran Grand Slam da gasar Olympics

Mahaifiyar Andy Murray, Judy ta ce danta zai samu karin nasarori a shekara ta 2013, kana ta yaba da tasirin da Kociya Ivan Lendl ya yi a kan sana'ar dan nata.

Murray ya samu nasarar da bai taba samun irin ta ba a wannan shekarar kasancewar ya ci zinare a gasar wasannin motsa jiki na duniya da aka yi, da kuma nasarar da ya samu a gasar Grand slam ta US open da Wimbledon

Mahaifiyar Murray ta ce shekara ta 2012 muhimmiya ce ga dan nata, kuma nasaraorin da ya samu sun kara masa kwarin gwiwa.