Keshi bai da mu da fushin da Odemwingie ya yi ba

Image caption Stephen Keshi Mai bada horo na Najeriya

Mai bada horo na Kungiyar kwallon kafa ta Najeriya, Stephen Keshi ya ce bai da mu ba da kalaman nuna damuwa da dan wasannan Peter Odemwingie ya yi ba saboda ya cireshi daga tawagar 'yan wasan Super Eagles da za su buga gasar cin Kofin Nahiyar Afrika ba.

Dan gaban West Brom ya mayar da martani zazzafa kan cireshi da akayi yana cewa anyi hakan ne saboda yana furtar albarkacin bakin sa kan yadda ake gudanar da harkokin wasanni a Kasar.

A wani sakon Twitter da dan wasan mai shekaru talatin da daya ya aika, ya ce " saboda ina magana kan batutuwan da ba ayi su daidai ba, ina ganin wasu ba sa jin dadin yadda nake yi."

Amma Mai bada horon Stephen Keshi ya ce bai da mu ba ko kadan da kalaman da dan wasan ya fada ba.

A cewar Mai bada horon Najeriya na da 'yan wasa da dama kuma ba zai yiwu a ce an gayyato ko wane dan wasa ba.

Karin bayani