Rovers ta kori mai bada horonta

Image caption Henning, Kochiyan da Rovers ta kora

Kungiyar kwallon kafa ta Blackburn Rovers ta kori mai bada horo na kulob din Henning Berg kwanaki hamsin da bakwai da kama aiki.

Mai bada horon mai shekaru arba'in da uku ya maye gurbin Steve Kean ne ranar 31 ga watan Oktoba, amma kulob din ya ci wasa daya ne kacal cikin wasanni goma tsawon wannan lokaci.

Tsohon dan wasan bayan Rovers, dan kasar Norway ya jagoranci wasa na karshe ne da Middlesbrough inda ta lallasa su da ci daya mai ban haushi a washegarin ranar Kirsimeti.

Kulob din dai ya fara ganawa da wadanda a cikinsu ake tsammanin za a dauki wanda zai maye gurbin tsohon mai bada horon, kuma Kulob din na fatan bada sanarwa nan kusa.

Karin bayani