Ferguson na farin ciki da Manchester United

Sir, Alex Ferguson
Image caption Sir, Alex Ferguson ya so a ce karawarsu da Newcastle ita ce taka leda ta karshe a kakar wasannin

Manajan kulob din Manchester United, Sir Alex Ferguson ya nuna farin ciki da rawar da kulob din ya taka na doke Newcastle.

Ferguson ya bayyana cewa 'yan wasan sun nuna kwarewa irin na zakaru, bayan kulob din ya doke Newcastle da ci hudu da uku a filin wasa na Old Trafford.

Nasarar ta daga likkafar kulob din a gasar Premier League, inda kulob din a yanzu ya sha gaban Manchester City da ta sha kaye a hannun Sunderland.

"Babu damuwa game da inda muka samu kanmu a gasar, amma fa mun nuna kwarewa irin na zakarun wasa." Ferguson ya furta haka cikin farin ciki.

Ya kara da cewa "Mun yi kasa da maki biyu a karawarmu da Swansea ranar Lahadi, amma mun cike wannan gibin a yanzu."

Dan yankin Scotland din ya kuma yi nuni da cewa " Ina ganin wasan ya kara mana kwarin guiwa, domin mun taka rawar a zo a gani a wasannin da muka buga."

Kulob din Newcastle ne dai ya fara zura kwallo a ragar Man U kafin a tafi hutun rabin lokaci, wanda James Perch ya ci.

Sai dai Jonny Evans ya rama, kafin dan wasan bayan dan kasar Ireland ya zura kwallon a cikin ragar kulob dinsa.

Da fari ba a amince da kwallon ba, amma daga bisani an amince, abin da kuma ya fusata Ferguson, wanda ke ganin ba a yi musu adalci ba.

Amma gab da kammala wasan, Javier Hernandez wanda ya maye gurbin Weyne Rooney, ya zura kwallon da ya baiwa Man U narasa a taka ledar.