Muna fata Demba Ba zai zauna —Pardew

Demba Ba
Image caption Newcastle na fata Demba Ba ba zai je ko ina ba

Kocin Newcastle, Alan Pardew, ya ce har yanzu bai fitar da tsammani ba cewa Demba Ba zai ci gaba da taka wa kungiyar leda bayan watan Janairu.

Ranar Lahadi wakilan dan wasan gaban dan asalin kasar Senegal suka tattauna da Chelsea; tattaunawar da daga baya aka ce ba ta yi armashi ba.

A kwantiraginsa da Newcastle akwai ayar kyale Ba, dan shekaru ashirin da bakwai da haihuwa, ya kama gabansa a kan kudi fam miliyan bakwai, kuma za ta fara aiki ne ranar 1 ga watan Janairu.

Pardew ya shaidawa BBC cewa: "Ina ganin yiwuwar zamansa na kankankan da yiwuwar tafiyarsa. Kuma ina fata zai zauna a wannan lokacin".

A 'yan watannin nan dai Newcastle ta yi ta kokarin cimma wata sabuwar yarjejeniya da Ba wadda za ta kai ga cire waccan ayar, kuma har yanzu ana musayar ra'ayi.

Karin bayani