Za a sabunta kwantiragin Lampard kuwa?

Frank Lampard
Image caption Frank Lampard ya ce yana jin dadin wasa a Chelsea

Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, Frank Lampard, ya ce babu alama za a tsawaita kwantiraginsa duk da kwazon da ya nuna a Stamford Bridge.

Dan wasan na tsakiya mai shekaru talatin da hudu a duniya na da dama ya kulla yarjejeniyar share-fage da wata kungiyar ketare a watan Janairu.

"A makwanni biyun da suka wuce, ba mu tattauna sabon kwantiragi ba", inji Lampard, wanda ya ci wa Chelsea kwallayenta biyu wadanda da su ta yi nasara a kan Everton da ci biyu da daya ranar Lahadi.

Cin wadannan kwallaye biyu da Lampard ya yi dai na nufin saura kwallo daya ya kamo dan wasa na biyu a jerin wadanda suka fi ci wa kungiyar ta Chelsea kwallaye—Kerry Dixon, wanda ya zura kwallaye 193. Wanda ke kan gaba shi ne Bobby Tambling, wanda ya ci kwallaye 202—kwallaye goma ne tsakaninsa da Lampard.

Bayan ya samu shiga kundin tarihin kungiyar ta Chelsea, Lampard ya yi iya kokarinsa a wasanni na baya-bayan nan don nuna cewa yana da rawar da zai taka a makomar kungiyar nan gaba.

Ya dai ce yana farin cikin kasancewa a tawagar da ta lashe wasanninta na baya-bayan nan na Gasar Premier guda hudu a karkashin jagorancin kocin riko Rafael Benitez.

Karin bayani