Najeriya ta fitar da rai kan Ameobi

Image caption Shola Ameobi, dan gaban Newcastle

Najeriya ta fitar da rai ga me da shigar dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Newcastle Shola Ameobi gasar cin kofin Nahiyar Afrika na shekara na 2013, bayan da ya ki daukar wayar su.

Mai bada horo na tawagar 'yan wasan na Najeriya Stephen Keshi ya sa sunan dan wasan a cikin 'yan wasan da ake sa ran za su buga gasar.

Amma daga bisani mai bada horo na Kulob din Newcastle, Alan Pardew ya bada sanarwar cewa dan wasan ba zai je Afrika ta kudu ba.

Ameobi, ya bayyana a watan Nuwamba a wasan sada zumunta da Venezuela kuma Stephen Keshi ya yi fatan dan wasan zai buga wasan gasar cin kofin Nahiyar Afrika wadda za a fara ranar sha tara ga watan Janairun bana.

Karin bayani