Sergio ba zai buga wasa da Arsenal ba

Sergio Aguero
Image caption Sergio Aguero na cikin 'yan wasan da suka zura wa Manchester City kwallaye 10 a ragar abokan karwarta a kakar wasannin da ake ciki

Kulob din kwallon kafa na Manchester City ya nuna fargabar cewa dan wasan gaban nan Sergio Aguero ba zai samu buga wasa a karwarsu da Arsenal ba.

Hakan dai ya biyo bayan sagewar kafa da yake fama da shi.

Man City za ta kara da Arsenal ne a wata taka ledar dake da muhimmanci sosai, a filin wasa na Emirate a ranar 13 ga watan janairun da muke ciki.

Sergio dai ya dingisa ya fita daga fili, bayan buga fenariti a gasar da Man City ta kara da Stoke a ranar Talata, inda aka tashi da ci uku da nema.

Haka kuma dan kasar Argentinan ba zai samu taka leda a karawar da Man City za ta yi da Watford ba, a zagaye na uku na gasar cin kofin FA da za a yi ranar Asabar.

"Da wuya ka iya bayyan girman raunin, sai dai kamar yadda ya sha faruwa kuma muka gani a baya, da wuya Sergio ya samu shiga wasanmu da Arsenal" Inji mataimakin mai horar da 'yan wasan Man City, David Platt.

Ya kara da cewa "Kafar za ta yi ta kumburi, kuma za dan fitar da jini, saboda haka a cikin kwana biyun nan, ba za mu iya cewa ga tsawon lokacin da zai dauka yana jinya ba. "

Sai dai manajan kulob din Roberto Mancini na ganin babu wata damuwa. "Ba na jin rauni ne mai girma, sharabarsa ta yi tsami, amma zai iya samun sauki a cikin kwana goma.