Habasha ta kammala kan 'yan wasa

Image caption 'Yan wasan Habasha

Kasar Habasha ta fitar da sunayen tawagar 'yan wasan da za su buga mata gasar cin kofin Nahiyar Afrika.

Mai bada horon 'yan wasan Habasha, Sewnet Bishaw, ya sanya dan tsakiyar nan haifaffen Kasar Sweden Yusuf Salah a cikin tawagar 'yan wasan.

Salah wanda aka bada aronsa ga Kungiyar kwallon kafa ta Syrianska dake Sweden, na daya daga cikin 'yan wasa uku dake wasansu a kasashen ketare a cikin tawagar.

Tawagar ta Bishaw galibinsu an dauko su ne daga kulob guda biyu a Habasha, tara daga ciki 'yan Saint George zakarun shekara 2012; takwas kuma daga Dedebit.

Habasha dai na rukucin C, inda za ta kara da Burkina Faso da Najeriya da kuma Zambia.

Karin bayani