Balotelli ya yi artabu da Mancini

  • 3 Janairu 2013
Image caption Mancini ya cukumi Balotelli

Dan wasan gaban nan na Manchester City Mario Balotelli ya yi artabu da mai bada horo Roberto Mancini a filin wasa na kulob din.

A wasu hotuna da aka fitar wadanda aka dauka ranar Alhamis sun nuna yadda 'yan wasa ke raba su a filin Carrington.

Kulob din dai bai ce uffan ba kan artabun.

Mancini dai zai fuskanci tambayoyi kan abin da ya faru a taron manema labarai da zai yi ranar Jumaa da safe.

A daya daga cikin hotunan an nuna Mancini ya ja rigar Balotelli, a wani hoton kuma ana kokarin hana shi tun karar dan wasan.

A watan Disamban bara ne Balotelli ya kai karar kulob din, kan cin tarar albashinsa na makonni biyu, daga bisani ya janye karar ya kuma karbi hukuncin.

Karin bayani