Demba zai koma Chelsea-Pardew

Image caption Demba Ba, na shirin komawa Chelsea

Mai bada horo na Newcastle United Alan Pardew na sa ran dan wasan gaban nan Demba Ba zai kammala shirin komawa Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ba tare da wata matsala ba.

Ba, mai shekaru 27 an bashi damar tattaunawa da Chelsea, kuma Alan Pardew ya shaidawa BBC cewa komawar dan wasan Chelsea zai yiwu.

Pardewa ya ce Demba Ba, ya yi musu kokari kuma suna yi masa fatan alheri.

A watannin baya dai Newcastle ta yi yunkurin daidaita wa da dan wasan don sabunta kwantiraginsa amma lamarin bai yiwu ba.

Karin bayani