Keshi ya soki farare masu horar da 'yan wasa

Stephen Keshi
Image caption Keshi ya kuma koka game da halayyar hukumomin wasan kwallo a nahiyar Afrika

Mai horar da 'yan wasan Najeriya, Stephen Keshi ya yi kakkausar suka game da rawar da fararen fatar dake horar da 'yan wasan Afrika ke taka wa.

Hakan na zuwa ne 'yan makonni kafin fara gasar cin kofin zakarun nahiyar Afrika.

Herve Renard Bafaranshe ne kuma shi ne ya jagoranci Zambia ga daukar kofi a gasar da aka yi a shekarar 2012.

Sai dai Keshi ya nuna damuwarsa ne game da wasu fararen fata dake horar da 'yan wasa a nahiyar Afrika.

"Fararen fata na zuwa Afrika ne kawai saboda kudi." Inji manajan kungiyar kwallon Najeriya.

"Ba sa yin wani abu daban da mu bama yi, ni ba mai nuna wariyar launin fata bane, amma dai haka batun yake. " A cewarsa.

Sai dai mai horar da 'yan wasan Uganda, Bobby Williamson bai amince da hakan ba.

Inda ya shaida wa BBC cewa "Ban taba zuwa nahiyar saboda kudi ba, na zo ne saboda aikin, domin fuskantar wani sabon yanayin sanin makamar aiki, kuma domin in yi aiki a sabon wuri, sannan ban taba nadama kan hakan ba."

Ya kara da cewa "A lokacin da na zo nan kudin da ake biya na bai wuce kudaden da zan biya kudin gida ba, yanzu abubuwa sun inganta saboda na samu nasarori."

"Kamar a gasar cin kofin Cecafa na yankin Afrika, kuma akwai lokacin da muka je gab da cin kofin gasar zakarun nahiyar Afrika."

Ya kara da cewa "Dukkaninmu muna da tamu kwarewar, kuma idan Keshin ya samu aiki mai gwabi-gwabi a nahiyar Turai, na san ba zai yi wata-wata ba zai zo ya karba."