'Armstrong zai nemi gafara a kan amfani da kwayoyin kara kuzari'

Image caption Lance Armstrong

Jaridar New York Times ta ce shahararren dan tseren keken nan, Lance Armstrong, zai nemi gafara a bainar jama'a a kan tu'amali da kwayoyin kara kuzari lokacin gasar tseren keke.

Jaridar ta ce Armstrong, mai shekaru 41, zai bayyana amincewarsa da wani rahoton bincike da hukumar da ke yaki da masu tu'amali da miyagun kwayoyi ta Amurka ta yi, wanda ya same shi da laifin yin amfani da kwayoyin da ke kara kuzari.

Hukumar ta kama Armstrong da takwarorinsa na Amurka da abin da ta bayyana cewa '' wani tsari da aka yi cikin hikima na amfani da kwayoyin da ke kara kuzari da ba a taba ganin irinsa ba a tarihin wasa a duniya''.

Lamarin ya sanya an kwace kambunsa guda bakwai na Tour de France, kana aka haramta masa shiga gasar tseren keke har abada.

A baya dai Armstrong ya ki bai wa hukumar binciken hadin kai, sannan ya sha musanta cewa ya yi amfani da kwayoyi masu kara kuzari.

Tun da aka haramta masa shiga gasar, Armstrong, bai ce uffan ba kuma bai shigar da kara game da lamarin ba.