Blatter bai amince da Boateng ba

sepp blatter
Image caption Blatter bai amince a fice daga fili kan wariyar launin fata ba

Shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya, FIFA, Sepp Blatter bai amince da matakin ficewa daga filin wasa da wadansu 'yan wasa ke dauka ba sabo da nuna musu wariyar launin fata.

Shugaban yana son daukan hukunci mai tsanani a kan lamarin, maimakon 'yan wasa su bar filin wasa.

A ranar Alhamis ne batun nuna wariyar launin fatar da ficewa daga filin wasan ya kara bayyana karara lokacin da dan wasan AC Milan, Kevin-Prince Boateng ya jagoranci 'yan wasan kungiyar tasa suka kauracewa filin wasa a yayin wasan sada zumuntar da suke yi da kungiyar Pro Patria lokacin da magoya bayan klub din Pro Patrian suke rera wakokin nuna wariyar launin fata.

Sabo da hakan ne dan wasan ya fice daga fili abokanan wasansa suma suka bi shi, kuma daga baya ya bayyana cewa ya dauki wannan mataki ne domin ya nunawa duniya cewa lalle fa abubuwa ba zasu ci gaba da kasancewa a haka ba a wannan lokaci.

Sai dai game da wannan mataki na Boateng din an ruwaito shugaban Hukumar ta FIFA, Sepp Blatter yana cewa, shi kam baya ganin ficewa daga filin abu ne da zai kawo karshen lamarin.

Ya ce yana ganin kamata ya yi a bullo da hukuncin ragewa duk wata kungiya da magoya bayanta suka aikata laifin maki ko kuma wani hukunci makamancin wannan.

Karin bayani