Swansea da Arsenal za su sake karawa

karawar Arsenal da Swansea
Image caption za a sake wasan Arsenal da Swansea

Kungiyar Kwallon kafa ta Swansea za ta sake karawa da Arsenal bayan da kungiyoyin biyu suka tashi canjaras biyu da biyu a wasan da suka yi na zagaye na uku na cin Kofin Kalubale na Ingila, FA, a filin wasa na Liberty.

Dan wasan Swansea dan kasar Spaniya, Michu wanda ya shigo wasan daga baya shi ne ya fara jefa kwallo a ragar Arsenal ana minti na 58 da hakan ya baiwa Swansea damar ja gaba a wasan.

Lukas Podolski ya ramawa Arsenal a minti na 81, kuma minti biyu tsakani sai Kieran Gibbs ya sake ciwa Arsenal kwallo ta biyu a minti na 83.

Sai dai kuma dan wasan Swansea Danny Graham a minti na 87 ya ramawa kungiyarsa inda aka tashi daga wasan canjaras biyu da biyu da hakan ta sa sai an sake karawar.