Takaitaccen tarihin kwallon Ivory Cost

Drogba
Image caption Didier Drogba ne jagoran tawagar ta Ivory Coast

Idan akwai wata kasar Afriaka da za ta karawar gani a gasar ta bana, to masana na hasashen Ivory Cost ce ganin irin kwararrun 'yan wasan da take da su.

Sai dai tana na da kalubale a gabanta ganin yadda ta kasa kai labari a gasar da ta gabata ba.

Kasar bata fuskanci wata matsalaba a kan harya ta ta zuwa Afrika ta Kudu, inda babu wata kasa da tayi nasara akan ta.

Shahararrun 'yan wasan da za su jagoranci kasar sun hada da gwarzon dan kwallon kafa na Afrika Yaya Toure na Manchester City da Didier Drogba.

Wani kalubale da ke gaban kociyan kasar, shi ne na kasancewar hankali zai karkata kansu, kamar yadda aka yi a gasar da ta gabata.

Sai dai sun yi alkawarin ba mara-da-kunya.

Za dai su kara ne da kasashen Algeria da Tunisia da kuma Togo a rukunin D.

Kuma ana yiwa wannan rukunin kallon wanda ya fi kowanne hatsari ganin irin kwararrun kasashen da ke ciki.

Zambia ce ta doke Ivory Coast a bugun fanareti na wasan karshe a gasar da ta gabata.