Mikel Obi ne gwarzon Najeriya

obi_mikel
Image caption Mikel Obi ya zama gwarzon dan wasan Najeriya

Dan wasan Chelsea Mikel Obi ya zama gwarzon kwallon kafa na Najeriya na 2012, a wata kuri'a da shafin wasanni na Intanet na Goal.com ya gudanar a Najeriya.

Mikel ya sami kashi 36.82 cikin dari na kuri'un da masu ziyartar shafin suka kada, Victor Mosses ya zama na biyu da kashi 26.35 cikin dari, Ahmed Musa na CSKA, shi ya zo na uku da kashi 20.28 cikin dari, ya yin da Reuben Gabriel na Kano Pillars ya zo na hudu da kashi 9.37 na kuri'un.

John Utaka na Kungiyar Montpellier ya sami kashi 6.82 na kuri'un ya yin da yake kokrin farfado da wasansa inda ya sami nasarar daukar kofin Gasar Lig ta Faransa.

Masu zaben sun zabi Mikel ne sabo da nasarar daukan Kofin zakarun Turai da kuma Kofin Kalubale na Ingila da kungiyarsa ta yi.

Karin bayani