AC Milan na shakkun daukar Guardiola

pep guardiola
Image caption AC Milan na shakkun daukar Pep Guardiola

Kungiyar Kwallon kafa ta Italiya AC Milan ta nuna shakkun daukar tsohon kocin Barcelona Pep Guardiola.

Kungiyar ta AC Milan na daga cikin kungiyoyin da ake yada jita-jitar cewa za su nemi Guardiolan.

Shugaban Kungiyar ta AC Milan Silvio Berlusconi, shi ne ya nuna shakkun daukar kocin domin maye gurbin mai horadda 'yan wasan kungiyar na yanzu Massimiliano Allegri, wanda Berlusconin ya ce ba shi da tabbacin zai ci gaba da kasance wa a Milan din a kakar wasanni ta gaba.

Berlusconi ya ce ya dade yana kokarin ganin ya kawo Guardiola AC Milan sabo da yadda Barcelona take wasa da kyau karkashin jagorancinsa, to amma tun daga shekarar da ta wuce AC Milan ta sami gwanaye da za su iya wasa da kyau kama yadda Guardiola yake yi sabo da haka yuwuwar zuwansa klub din yanzu ta ragu matuka.

Berlusconi ya kuma bukaci magoya bayan kungiyar da su kara hakuri da klub din sabo da matasan 'yan wasa ta ke da su yanzu inda ya ce sai nan da shekara biyu zuwa uku za a fara ganin tasirinsu.

Ya ce suna kokarin sake gina kungiyar ne yanzu sabo da basa son dan wasan da ya wuce shekara 21.

Yanzu AC Milan tana matsayi na bakwai ne a gasar Serie A ta kasar Italiyan da maki 30 a wasanni 19.

Karin bayani