Berlusconi ba ya sha'awar Balottelli

silvio berlusconi
Image caption Silvio Berlusconi ya ce AC Milan ba ta neman Balotelli

Shugaban Kungiyar AC Milan Silvio Berlusconi ya musanta rade radin da ake yi cewa klub din zai sayi Mario Balotelli, inda ya bayyana dan wasan da wasu ke yi wa kallon takadari mai wuyar sha'ani da cewa '' rubabbiyar tuffa ce''.

Berlusconi ya ce ''ko alama Balotelli ba ya gabana, baya cikin tunanina, ya zama rubabbiyar tuffa da duk inda ka sanya ta zata bata sauran ko da kuwa kungiyar Milan ce''.

A baya an sha rade radin cewa AC Milan din zata sayi Balotelli dan shekara 22 domin maye gurbin Alexandre Pato da Robinho.

A ranar Alhamis ne Balotellin da kocin kungiyarsa ta Manchester City Roberto Mancini suka cukumi juna sakamakon wata sa-in-sa a lokacin atisaye.

Sai dai kuma a wani wasan sada zumunta da 'yan wasan Manchester City 'yan kasa da shekara 21 suka yi ranar Litinin da Blackburn Balotelli ya ci kwallaye biyu daga cikin hudu da City din ta jefa a raga.

A wasan da Cityn ta yi da Watford na zagaye na uku na cin Kofin Kalubale na Ingila ma an sanya dan wasan na wani dan lokaci inda klub din ya sami nasara a kan Watford da ci 3-0.

Ana ganin Man city din tana kokarin dawo da dan wasan kan ganiyarsa ne domin buga wasan da zata yi da Arsenal ranar Lahadi sabo da Sergio Aguero ya na jiyya.

Karin bayani