Tarihin Super Eagles na Najeriya

Super Eagles na Najeriya
Image caption A baya-bayan nan kungiyar bata taka rawar gani yadda ya kamata

Kodayake ta shiga wasu wasannin kasa da kasa, sannan kuma ta dauki kofin nahiyar Afrika a shekarun 1980 da 1994, Najeriya ta yi fice a fagen tamaula na kasashen duniya a shekarar 1986 bayan ta dauki kofin FIFA na 'yan kasa da shekaru 17.

Tun daga nan ne kuma, tauruwar kasar ta fara haske a fagen kwallon kafa, kodayake kimarta ta fara rauguwa a baya-bayan nan.

Kasar za ta iya bugun girji da 'yan wasan da sunanyensu suka yi zarra kamar tsohon dan wasan gaba na Arsenal wato Kanu Nwankwo da dan wasan tsakiya Jay-Jay Okocha da kuma Rashidi Yekini.

Kungiyar kwallon kafar kasar dai ba ta samu nasarar shiga gasar cin kofin nahiyar Afrika da aka yi na karshe, wanda Gabon da Equatorial Guinea suka dauki bakuncinsa.

Kungiyar Super Eagles wacce manajanta dan kasar ne, Stephen Keshi, na burin kaiwa zuwa akalla zagaye na kusa da na karshe, a gasar cin kofin nahiyar Afrika da kasar Afrika ta Kudu za ta dauki bakuncinsa.

Shahararrun 'yan wasa

Najeriya dai ta samu shiga gasar ta bana ce bayan ta samu jimillar kwallaye takwas da uku tsakaninta da Liberia, a zagayen karshe na wasannin neman share fage.

Kuma ana ganin sun kuduri aniyar wuce wa zagayen wasannin rukuni-rukuni na gasar.

Kungiyar dai na rukunin C kuma za ta kara ne da Zambia da Burkina Faso da kuma Habasha.

Kuma babban aikin da ke gaban Super Eagles shi ne na wucewa gaban kasar da ke kare kambunta wato kungiyar Chipopolo ta Zambia, don nuna cewa ta dawo da karfinta.

'Yan wasan kulob din Celsea John Mikel Obi da Victor Moses da kuma kyaftin din kungiyar wato tsohon dan wasan baya na Everton, Joseph Yobo sune zakarun 'yan wasan da kasar ke fatan za su kaita ga gaci.

Kodayake rashin sanya sunan dan wasan gaba na West Brom, Peter Odemwingie a cikin tawagar kasar ya janyo kalaman bacin rai daga dan wasan a shafinsa na Twitter, hakan bai dauke hankalin shirin tawagar ba.

Sannan 'yan wasa biyu da ke zaune a Ingila Shola Ameobi da Danny Shittu ba su amsa goron gayyatar kasar ba, saboda wasu uzuri na kulob- kulob din da suke buga wa wasa.

Duk da rashin nasarar da Super Eagles ta samu a baya, wanda ya isa ya sa mutum ya cire son kungiyar a ransa, da dama an yi amanna cewa wasan kwallo na ci gaba da kasancewa wani abu tilo da ke hada kan 'yan Najeriya duk da banbancin addini da na kabilanci.

Karin bayani