Magoya bayan Real sun gaji da Mourinho

jose mourinho
Image caption Jose Mourinho na shan matsi daga magoya baya

Wata kuri'ar jin ra'ayin magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid da aka gudanar ta nuna cewa wasu daga cikin su sun gaji da yadda Jose Mourinho ke tafiyar da klub din.

Wata jaridar wasanni da ke goyon bayan Real Madrid a Spaniya mai suna Marca ita ce ta gudanar da kuri'ar a kan magoya bayan kungiyar 704 kafin wasan ranar Lahadin da ta gabata wanda kungiyar ta sami nasara a kan Real Sociedad.

Yayin da kashi 54.4 cikin dari na magoya bayan suka amince kocin ya ci gaba da zama a kungiyar kashi 41.8 cikin dari suna ganin yakamata ya tafi.

Kashi biyu bisa uku na magoya bayan Real Madrid din suna ganin yadda mai horadda 'yan wasan yake tafiyar da harkokin klub din yana ciyar da shi baya.

Kimar da magoya bayan suke baiwa kocin daga kashi 8.82 cikin goma a watan Maris na 2011 ta ragu yanzu zuwa kashi 6.68.

Real Madrid din dai ta na bayan babbar abokiyar hamayyarta Barcelona a gasar La Liga da maki 16.

Magoya bayan sun yiwa tsohon kocin na Porto da Chelsae da kuma Inter Milan dan shekara 49 eho lokacin da aka bayyana sunansa kafin fara wasansu da Real Madrid ranar Lahadi.

Mourinho ya fusata magoya bayan klub din da dama saboda kin sanya babban maitsaron gidan kunigyar Iker Casillas da ya yi a wasa karo biyu a jere.

Kocin ya sha alwashin ba zai bar mukamin nasa ba sakamakon rashin nasarar da Madrid din ta yi da ci 3-2 a karawarta da Malaga a watan Disamba.