Yabon Van Persie ya zaburar da Tevez

carlos tevez
Image caption Carlos Tevez zai yi kokari City ta dauki Premier

Dan wasan Manchester City Carlos Tevez ya ce yabon da kocinsu Roberto Mancini ya yi wa Robin Vern Persie na Manchester United ya zaburar da 'yan wasan gaba na Cityn.

A kwanakin nan ne dai Mancinin ya bayyana nadamarsa ta rashin sayen Van Persie wanda ya zuwa yanzu ya ciwa Manchester United kwallaye 20 inda ya ce dan wasan shi ne bambamcin dake tsakanin kungiyoyin biyu.

Tevez wanda ya ciwa City kwallaye 8 a bana ya ce wadan nan kalamai sune suka karfafa wa 'yan wasan na City guiwa.

A don haka ya ce zai taimaka domin su sami nasarar daukar kofin gasar Premier da na Kalubale baki daya.

Zakarun gasar ta Premier, City, yanzu suna bayan abokanan hamayyarsu United da maki 7 ya yin da wasanni 17 suka rage a kammala gasar Premier ta bana, bayan da Cityn ta yi rashin nasara a karawarsu da United din a gida ranar 9 ga watan Disamba.

Ranar 6 ga watan Afrilu ne kungiyoyin za su sake haduwa a Old Trafford, a kan haka Tevez din ya ce da sauran lokaci da kuma wasanni kafin wannan haduwa, kuma ya ce wani abu da gasar ta Premier shi ne gasa ce da sai ta kare ake sanin zakaranta, a don haka United ta sani ce idan ta yi rashin nasara a wasa daya ta san tazarar da ke tsakaninsu za ta ragu sosai. Sun kwana da sanin haka inji shi.

Tevez ya kara da cewa a bara ma haka muka yi ta fafatawa ,United ta yi rashin nasara a wasu wasanni mu kuma muka farfado har muka sami nasarar daukan kofi.

A baran dai Manchester United ta baiwa City tazarar maki takwas amma ta tarar da ita ta dauki kofin da bambamcin yawan kwallaye.

Karin bayani