Man United ta lallasa Liverpool 2-1

'yan wasan United da Liverpool
Image caption Manchester United ta lallasa Liverpool a gida

Kungiyar Manchester United ta cigaba da kasance wa kan gaba a gasar Premier bayan da ta ci abokiyar hamayyarta Liverpool 2 - 1 a Old Trafford.

Robin Van Persie ne ya fara ci wa United kwallonta a dai-dai minti na 19 da fara wasa.

A mintuna 54 da wasan ne kuma bayan an dawo daga hutun rabin lokaci Nemanja Vidic ya sami nasarar jefa kwallo ta biyu a ragar Liverpool.

Sa dai mintina uku tsakani ne kuma wato a minti na 57 Liverpool ta rama kwallo daya ta hannun Daniel Sturridge.

Da wannan nasara yanzu United tana da maki 55 a wasanni 22 inda ta ci gaba da zama ta daya a gasar ta Premier, yayin da ita kuma kungiyar Liverpool ta ci gaba da kasancewa da maki 31 daga wasanni 22.

Karin bayani