Vincent Kompany ya kare kansa

Vincent Kompany
Image caption Kyaftin din Manchester City, Vincent Kompany na barin filin wasa

Kyaftin din kulob din Manchester City, Vincent Kompany ya kare kokarin karbe kwallo da yayi a karawarsu da kulob din Arsenal, lamarin da yasa aka kore shi.

Alkalin wasa Mike Dean ne ya kori Kompany mai shekaru 26 a kan dan wasan tsakiya na kulob din Gunners wato Jack Wilshere.

Kuma an ba kompany jan katin ne, bayan an dawo daga hutun rabin lokaci, a wasan da aka tashi ci biyu da nema.

Kyaftin din ya rubuta a shafinsa na Twitter cewa "Idan abokin hamayya ya kawo farmaki a filin wasa, kuma ka yi kokarin kare wa, to dole ne a gwara."

Da aka tambayi manajan kulob din na City, Roberto Mancini ko za su kalubalanci korar da aka yiwa Kompany, sai ya ce "Kwarai kuwa."

Mancini ya kara da cewa "Za mu daukaka kara, kuma ina ganin za muyi nasara saboda abu ne mai sauki domin yadda lamarin ya kasance kenan."

Sai dai manajan ya koka game da cewa kulob din na fuskantar matsala saboda rashin 'yan wasa, kuma ga shi Kyaftin din ba zai buga wasanni uku ba.

Mancini yace yana ganin alkalin wasan ya yi kuskure.

Amma kuma shi Kompany bai dora laifin kan alkalin wasan ba.

Karin bayani